Rayuwar offentlig
[search 0]
Mer
Download the App!
show episodes
 
Loading …
show series
 
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan tsananin zafin da ake fama da shi a wasu yankuna na Nahiyar Afirka, a wannan shekarar ya tsananta inda a wasu sassa na tarayyar Najeriya lamarin ya dan wuce misali. Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya, jiha ce da tun asali aka sani da tsanantar kowane juyin yanayi na Zafi ko na Sanyin Hunturu ko ma na…
  continue reading
 
Shirin na wanna makon zai yi dubi ne akan katafaren shirin zamanantar da aikin noma da gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta kaddamar. Masana na ganin Jihar a matsayin wadda idan aka tattala kasar noma da take da ita, a cikinta kadai za a iya noma abincin da zai iya ciyar da kasar har ma a iya fitarwa zuwa kasashen ketare. A wannan aikin da aka kaddama…
  continue reading
 
Shirin wannan mako zai ba da hankali ne a kan yadda Najeriya ta kasance akan gaba a fagen noman masara a daukacin yankin yammacin Afrika, inda kasar ke samar da sama da kashi 48 na masarar da ake nomawa a yankin. Mafi yawan masarar da ake nomawa a kasar, na fitowa ne daga yankin arewacin kasar, musamman jihohin Bauchi, Kaduna, Borno, Naija da Tarab…
  continue reading
 
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" a wannan mako na musamman ne, domin kuwa ya yi dubi ne a kan matsaloli da dama suka addabi bangaren noma a Najeriya, wanda ake ganin su suka hana kasar samarwa kanta abincin da zai wadata jama'arta musamman a wannan lokaci da ake fuskantar tsadar sa a kasuwanni. Shirin na dauke da rahotanni da kuma hirarraki daga sassa…
  continue reading
 
Shirin mu na wannan mako zai yi duba ne a kan batun yadda wasu suka rungumi sana'ar kiwon Dodon kodi a yankin Naja Delta da ke tarayyar Najeriya musamman a jahar Cross River. Wakilin mu dake yankin MURTALA ADAMU ya kai ziyara a wa ta Gona da ake wannan kiwon kuma ya zanta da wadanda suke sana'ar, wa ta da ta rungumi sana'ar ta yi bayani dalla dalla…
  continue reading
 
Shirin awannan mako zai maida hankali ne kan batun halin da yankunan da suka gamu da iftila’in ambaliya ke ciki a Najeriya, tare da duba matakan da suke dauka na kare kai anan gaba. Idan ba a manta ba dai Shekara guda kenan da faruwa mummunar ambiyar ruwa a wasu jihohin Najeriya, kuma jihar jigawa dake arewacin kasar na cikin jihohin da ambaliyar t…
  continue reading
 
A wannan mako shirin zai yi dubi ne akan shirin gwamnatin Najeriya na bunkasa noman alkama domin yaki da talauci da kuma wadata kasar da abinci. A wani mataki na kawar da matsalar zaman kashe wando da magance rashin aikin yi musamman tsakanin matasa, gwamnatin Nigeria ta kuduri aniyar amfani da noma wajen samar da guraben aikin yi wa dubban matasan…
  continue reading
 
Hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya wadda gwamnatin kasar tace yakan kai sama da Nera triliya 3 a kowacce shekara . Sashen Hausa na Radio France International ya yi tattaki zuwa jihar Kano a Najeriya inda muka gana da masu ruwa da tsaki domin jin yadda ta kaya a wannan karowandada suka kuma bayyana cewa anf…
  continue reading
 
Shirin wannan mako zai yi dubi ne yadda Hukumar da ke kula da harkokin hasashen yanayi ta Nigeria, ta yi hasashen samun wani gagarumin sauyin yanayi a yankunan arewa maso gabas da arewa ta tsakiya cikin ‘yan kwanaki masu zuwa. Bugu da kari hukumar, ta bayyana cewa shima yankin kudancin Nigeria zai shiga yanayi na zafin rana da wasu alamun hadari, k…
  continue reading
 
A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan batun hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya wadda gwamnatin kasar tace yakan kai sama da Nera triliya 3 a kowacce shekara . Sashen Hausa na Radio France International ya yi tattaki zuwa jihar Kano a Najeriya inda muka gana da masu ruwa da tsaki domin jin yadda ta k…
  continue reading
 
Shirin a wannan karo zaiyi dubi ne akan wasu bayanan kididdiga da suka yi nuni da cewa kakar noma ta shekara ta 2023, na daga cikin lokaci mafi muni ga mafi yawan manoman Nigeria a sakamakon matsalar sauyin yanayi da ta haifar da karancin ruwan sama. A halin yanzu dai, wata babbar kungiyar kasa da kasa mai suna Action Aid, ta bayyana cewa irin hasa…
  continue reading
 
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, a wannan mako ya yi dubi ne a kan gidauniyar kudade daya kai dalar amurka miliyan 70 da kasar Amurka da Norway zasu samar don inganta harkan noma a nahiyar Afrika. Kasashen biyu sun sanar da hakan ne a garin New York na kasar Amurka inda sukace kowacce a cikin su zata bada dala miliyan talatin da biya…
  continue reading
 
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, ya maida hankali ne kan yadda gwamnatin Najeriya karkashin ma'aikatar albarkatun ruwa da Bankin Raya Afrika suka horar da manoman karkara dabarun noma na zamani, wanda za su taimaka wurin yaki da dumamar yanayi da a yanzu duniya ke fama da shi wato Climate Change a turance.Wannan horo da aka baiwa wad…
  continue reading
 
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, ya maida hankali ne kan yadda 'yan kasuwa a Tarayyar Najeriya musamman arewacin kasar, ke shiga kasuwanni da makudan kudi domin saye kayayyakin abinci, su kuma boye domin jiran lokacin da kayan za su yi tsada a kasuwanni kafin su fara fitowa da su da zummar samun kazamar riba, ba tare da la'akari da m…
  continue reading
 
Shirin Muhallinka rauwarka tare da Nasiru Sani ya mayar da hankali ne kan sauyin yanayi wanda ya haddasa tsananin zafin da yanzu haka ya addabi kasashe da dama musamman a yankunan Turai nahiyar Asiya da kuma Afrika wada tuni ya haddasa gagarumar illa ta hanyar kafar da tarin koguna a mabanbantan yankuna. A bana kadai an ga tarin gobarar daji a kusa…
  continue reading
 
Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Nasiru Sani a wannan mako ya mayar da hankali ne kan hasashen masana kan yiwuwar daukewar ruwan damuna da wuri a wasu sassan Najeriya, lamarin da zai haddasa gagarumar matsala a tsarin samar da abinci. Wannan hasashe dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin samu…
  continue reading
 
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan mako zai yi duba ne kan batun matsalar takin zamani da manoma ke fama da shi a Najeriya shekara da shekaru, duk da cewa tsadar takin na bana ba irin wadanda aka saba gani a baya bane. Matsalar tsadar taki dai a yanzu ita ce ta fi ci wa manoma tuwo a kwarya a Najeriya. A latsa alamar sauti don sauraron cikakke…
  continue reading
 
A yau shirin zai bada hankali ne akan sakin ruwan madatsar ruwan lagdo da kamaru zata yi, wanda yanzu haka mazauna wasu yankuna da ruwan zai kwaranya ta cikin su a Najeriya ke cikin tashin hankali dangane da irin asarar kama daga ta rayuka har ya zuwa ta dukiyoyi. A karshe dai, gwamnatin Nigeria, ta tabbatar da cewa makwabciyarta Kamaru, ta sako ru…
  continue reading
 
Shirin ya karkata ne akan wani shirin tallafawa manoma a Najeriya wanda Bankin raya Afirka ke tallafawa kan yadda za’a samu inganci da habakar samar da wadataccen abinci a fadin kasar wato agricultural transformation agenda support program karkashin ma’aikatar noma ta kasar wanda aka kaddamar a garin Bunkuren jihar Kano.…
  continue reading
 
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" a wannan makon ya yi duba ne kan matsalolin zaizayar kasa, da ke samu a yankin Niger Delta da ke shiyar kudu maso kudancin Najeriya. Jahar Cross River na daya daga cikin jahohin da ke fama matsalar musamman a wani bangare na babban birnin ta Calabar. Wannan matsalar dai ta haifar da asarar rayuka da kuma dukiya mai tar…
  continue reading
 
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' a wannan karon ya yi nazari ne kan yadda a yanzu ake amfani da Kirkirarriyar Basirar Ai a bangaren noma da kiwo musamman a wannan lokaci da ake kokarin wadata duniya da abinci. Tuni dama dai kasashen da suka ci gaba suka dade wajen yin amfani da irin wannan fasahar don samarwa al'ummar su wadatatcen abinci. Sai dai duk…
  continue reading
 
Loading …

Hurtigreferanseguide

Copyright 2024 | Sitemap | Personvern | Vilkår for bruk | | opphavsrett